Jummaʼa 18 Satumba 2026 - 21:42
Ayoyin Rayuwa | Ku Saka Mummuna da Kyakkyawa

Hauza/ Yin haƙuri da mutane ba kawai kyawawan ɗabi’a ba ne, har ila yau hanya ce ta shiryarwa da kuma mayar da ƙiyayya zuwa abota. Labarin mutumin Sham da yadda Imam Hasan (A.S) ya kyautata mu’amala da shi, misali ne na musamman na wannan fasaha.

Kamfanin Dillancin Labaran Hauza | Ɗaya daga cikin muhimman shawarwarin addinin Musulunci shi ne yin haƙuri da mutane da kyautata mu’amala da su.

Alƙur’ani Mai Girma ya bayyana babban darajar wannan ɗabi’a da cewa:

«وَلَا تَسْتَوِي الْحَسَنَةُ وَلَا السَّيِّئَةُ ادْفَعْ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ فَإِذَا الَّذِي بَيْنَكَ وَبَيْنَهُ عَدَاوَةٌ كَأَنَّهُ وَلِيٌّ حَمِيمٌ.»

“Kyakkyawa da mummuna ba su zama daidai ba. Ka tunkuɗe mummuna da abin da ya fi kyau. A lokacin nan, sai ga wanda ke tsakaninka da shi akwai ƙiyayya, ya zama kamar masoyi na ƙwarai kuma na kusa.”(1)

Bayani:

A zahiri, ya kamata dukkan ayyukanmu su kasance masu ɗauke da alamar “shiriyar Allah.” Bai kamata mutum ya cika kansa da hasken shiriya kawai ba, a’a, ya kamata maganganunsa da ayyukansa su kasance ta yadda za su taimaka wajen shiryar da sauran mutane. Kuma wannan ba zai samu ba sai ta hanyar soyayya da ƙauna.

A wasu lokuta, mutane kan yi mana abubuwan da ba su dace ba. A irin waɗannan lokuta, akwai hanyoyi biyu na mu’amala.

Na farko shi ne mu mayar da mugun hali da mugun hali, wato mu rama abin da aka yi mana. Na biyu kuma shi ne mu kame kanmu a gaban mummunan aikin da wani ya yi, sannan mu nuna masa ƙauna.

Kamar yadda Imam Ja’afar Sadik (A.S) ya ce:

«صِلْ مَنْ قَطَعَكَ وَاعْفُ عَمَّنْ ظَلَمَكَ وَأَعْطِ مَنْ حَرَمَكَ وَأَحْسِنْ إِلَى مَنْ أَسَاءَ إِلَيْكَ.»

“Ka sadar da zumunci da wanda ya yanke hulɗa da kai; ka yafe wa wanda ya zalunce ka; ka ba wanda ya hana ka; kuma ka kyautata wa wanda ya yi maka mummuna.” (2)

Sakamakon irin wannan hali, kamar yadda Allah Madaukaki ya bayyana a cikin ayar da aka ambata, shi ne samar da abota da ƙauna.

Mutumin da a baya yake nuna maka ƙiyayya, zai iya, sakamakon yadda ka mayar da martani, ya koma masoyi kuma aminin da a wannan karon duk ƙaunarsa ta karkata zuwa gare ka.

A nan ne mutumin da ya kawata kansa da shiriya zai iya zama sanadin shiryar da wani mutum, ya kuma taimaka masa ya zauna a kan tafarkin Allah Madaukaki.

Mu’amalar Imam Hasan Mujtaba (A.S) da Wani Mutumin Sham

Wani mutum daga Sham ya ga Imam Hasan (A.S) yana kan abin hawansa. Sai ya tsaya a gabansa ya fara zagin sa. Imam Hasan (A.S) ya yi shiru, bai mayar masa da martani ba.

Bayan wannan matafiyi ya gama zagin da yake yi, sai Imam Hasan (A.S) ya gaishe shi, ya yi murmushi, sannan ya fara magana da shi, yana cewa: “Ya kai dattijo! Ina tsammanin kai baƙo ne. Wataƙila ka yi kuskure ne game da mu. Yanzu, idan ka nemi gafara da amincewarmu, za mu yafe maka.

Idan kana son wani abu, za mu ba ka. Idan kana neman girma da shiriya, za mu shiryar da kai. Idan kana buƙatar abin hawa, za mu ba ka shi. Idan kana jin yunwa, za mu ciyar da kai. Idan ba ka da tufafi, za mu tufatar da kai. Idan kana cikin buƙata, za mu biya maka buƙatarka. Idan an kore ka daga garinku, za mu ba ka mafaka. Idan kana da wata buƙata, za mu biya maka ita.

Yanzu ya fi dacewa ka kawo kayanka zuwa gidanmu, ka zauna tare da mu har zuwa lokacin da za ka kammala tafiyarka. Domin gidanmu yana da faɗi, kuma akwai abubuwan jin daɗi da kwanciyar hankali a cikinsa...”

Lokacin da mutumin Sham ya ji waɗannan kalmomi masu cike da ƙauna daga Imam Hasan (A.S), sai ya fara kuka, ya ce: “Na shaida cewa kai ne halifan Allah a doron ƙasa. Kuma hakika, Allah ne Mafi Sani game da inda Ya sanya saƙonninSa.”

“A baya, kai da mahaifinka kun kasance mutanen da na fi ƙi a cikin halittun Allah. Amma daga wannan lokaci, babu wani mutum da nake ƙauna fiye da ku.”

Sai mutumin ya ɗauki kayansa ya kai su gidan Imam Hasan (A.S), kuma ya kasance baƙonsa har zuwa lokacin da ya bar Madina. Ya kuma zama daga cikin mutanen da suka yi imani da ƙaunar wannan iyali.(3)

Madogara 

1. Suratul Fussilat, aya ta 34.

2. Biharul Anwar, juzu’i na 68, shafi na 423.

3. Manaƙib Ali Bn Abi Talib, juzu’i na 4, shafi na 19.

An shirya wannan bayani ne a Sashen Ilimi da Al’adu na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha